Ban Hakuri
Ina neman ahuwa daga wajen masu karatu saboda rashin kawo musu
kashi na biyar na kasidar da muka taso a baya mai take: "Tsarin Gadon
Dabi'u da Siffofin Halitta a Kimiyyance (Genetics)". Hakan ya faru ne saboda shagulgula da suka
min yawa cikin makon da ya gabata, bayan masassara da nayi fama da ita na wajen
kwanaki tara. Kuma ganin cewa ba kasida
ce da kawai zan farka daga barci in dauki alkalami da biro in kama rubutawa ba,
dole sai da bincike, sai na dakatar.
Domin kamar yadda hausawa ne ke cewa, "Zuwa da wuri (kudi) ya fi
zuwa da wuri (sammako)". A mako na
sama in Allah ya so za a ga ci gaba.
Amma wannan makon ya wuce sai dai a mini ahuwa. A yau za mu juya akala zuwa wani bangaren
kuma.
Yau za mu ci gaba ne da
kasidar da muka fara a cikin watan Afrailu mai take: "Rayuwar Matasanmu a
Dandalin Facebook." Wannan kasida
kamar hira ce, wacce ke dauke da fadakarwa, ba wai tonon silili ba, kan irin
dabi'unmu (har da ni kaina) wajen ma'amala da bayanai, da jama'a, da kuma yadda
muke siffatawa ko bayyana wa duniya rayuwarmu ta hanyar dandalin Facebook. A kasidar farko mun kawo misalai ne kan haka,
dangane da rayuwar matasan kasar Hausa a wannan Dandali. Da yawa cikin masu karatu sun yaba wancan
kasida, amma wasu basu ji dadinta ba. Na
kuma fahimci hakan ta hanyoyi da dama.
To amma, tunda kasidar bata ambaci sunan kowa ba, bata kuma nakalto
rubutun kowa ba, babu laifi. Manufa dai,
kamar yadda na sanar a baya, shi ne fadakarwa.
Gyara kayanka, inji
Malam Bahaushe, bai zama sauke mu raba.
Sai dai sabanin yadda nayi a baya inda na kawo misalai daga yadda
matasanmu ke mu'amala a dandalin, a wannan mako zan kawo misalai ne daga
kasashen da suka ci gaba a fannin sadarwa da tattalin arzkin kasa. Mu ga yadda wannan sabuwar hanya ta abota a
yanar gizo ke tasiri wajen tilasta wa matasa dai musamman, su kauce hanya, su tafka
katobarar da watakila har karshen rayuwarsu ba za su mance da ita ba. Hausawa na cewa, "Daga na gaba ake ganin
zurfin ruwa."
Manyan Katobara a Dandalin Facebook
A cikin wani taro da yayi da matasa, Shugaba Obama na kasar Amurka
yace: "Ina son in yi kira ga duk wanda ke wannan wurin (taro) cewa,
kowannenku yayi hankali da abin da yake rubutawa a Dandalin
Facebook." Me yasa Shugaba Obama
yayi wannan gargadi, a matsayinsa na Shugaban kasa? Dalilin haka na cikin sirrin dabi'ar dan adam
ne, na son sadarwa tsakaninsa da jinsinsa, ko ma wasu jinsin. Sannan dan adam
na da saurin mantuwa, musamman dai a wannan zamani mai cike da kayayyaki da hanyoyin
sadarwa masu shagaltarwa. Kowa na son a san shi wane ne, ko ita wance ce. Da
abin da ya kamata da wanda bai kamata ba, duk Allah Allah yake ya rubuta. Wannan shi ne abin da ya kai da yawa daga
cikin wasu har suka tafka katobara mafi girman gaske a Dandalin Facebook,
musamman ta la'akari da muhallin da suke rayuwa a ciki.
A kasar Jamus wata yarinya mai suna Tassa mai shekaru goma shabiyar
tayi rajista a Dandalin Facebook. Saboda
shagala da tayi da kuma zakin sadarwa tsakaninta da abokanta, rannan kwatsam
sai ta rubuta cewa rana kaza za ta cika shekaru 16 a duniya. Ita har ga
Allah ta rubuta ne kawai, ba wai don wasu su zo ba. Bata ma san hakan zai yi
wani tasiri ba. Abin ka da rayuwar turai
masu son biki, nan take gidan ya dinke da jama'a, daga masu goge sai masu rike
da molo, da garaya na zamani, suna ta rera wakoki, wasu rike da fure, wasu rike
da kyaututtuka. Da ta ga haka, sai wannan
yarinya ta fahimci katobarar da ta tafka, nan take ta gudu zuwa gidan Goggonta
ta buya. Matasa sun fi dubu a kofar gidan, kowa ya zo ya sha biki. Kwalelenku!
Daga cikin abin da ya kamata matashi ya rika la'akari shi ne,
rayuwa kamar madubi ne. Abin da ka yi a
baya, shi zai dada tabbatar da waye kai a rayuwarka ta gaba. Wannan shi ne sirrin da Ray Lam, wani matashi
a garin Vancouver na jihar British Colombia da ke kasar Kanada ya mance. Ray matashi ne da ya gama jami'a, ya kuma yi
ayyuka sosai wajen ganin ci gaban rayuwarsa. Ganin haka tasa yayi tunanin shiga
siyasa don kawo sauyi a mazabarsa. Nan take ya kama kamfe, jama'a suka ta
zagaye shi: "Sai kayi…sai ka yi…sai ka yi," kamar dai yadda ake wa 'yan
siyasarmu a yau. Ya shahara sosai har
abokan hamayyarsa suka fara neman yadda zasu kayar da shi, amma abu ya ci
tura. Sai ta hanyar Dandalin Facebook
suka ci nasara. Yana da shafi inda yake
kamfe a dandalin, wanda ke cike da hotunansa na zamanin samartaka. Daga ciki akwai wadanda ya dauka yana dafe da
nonon budurwarsa a gidan rawa ana holewa, da wanda ya dauka mai bayyana
al'aurarsa a yayin da wani abokinsa ke dafawa. Nan take suka dauko wadannan
hotuna suka ta rabawa, ana mannawa a wurare. Wannan ya rage masa shahara, da
cewa ashe dan iska ne, har yana bayyana tsaraicinsa ga duniya. Wannan bai kamata ya zama shugaba ba. Wannan ya tilasta masa fita daga jerin 'yan
takara, abokan hamayyarsa suka samu nasara a kansa. Babbar dalili shi ne katobarar da yayi wajen
dora hotunansa marasa kyau, masu nuna rayuwarsa ta baya, wanda hakan ya kai shi
ya baro.
Duk lalacewarka, muddin ka san nan gaba kana iya neman alfarma a
wajen mutum, to kada ka aibanta shi.
Babu wanda ya fi sanin darasin da ke karkashin wannan fadakarwa irin
Cameron Reily, daya daga cikin sojojin da ke gadin fadar sarauniyar Ingila a
kasar Burtaniya. Daidai lokacin da ake
ta kokarin shirya bukukuwan auren Yarima Williams da amaryarsa mai suna
Catherine, kowane soja daga cikin masu gadin yana son a ce yana cikin jerin
sunayen masu yin fareti don kayatar da wannan biki. Cameron Reily ya fara gyatta tufafinsa da
dokin hawansa, don samun shiga, sai kawai ya ji an ce an cire sunansa nan take.
Meye dalili? An shiga shafinsa na Facebook ne sai aka samu
inda yayi ta fadin wasu kalamai marasa da'a kan amaryar a baya, da cewa ba kowa
ba ce, kuma wa ma ya damu da ita! Wannan
shi ne abin da ya ci shi. Ashe kowa da
ranarsa.
A rayuwa idan za ka yi zancen wasa, to ka san irin wacce za ka yi,
kuma a ina za ka yi ta! In kuwa ba haka
ba, to, wani zancen wasan zai kaika ya baro.
Abin da ya faru kenan da wani matashin kasar Burtaniya, kwararren Akanta
mai suna Chambers. Watarana ya sayi
tikitin jirgi zuwa birnin Belfast don kai wa budurwarsa ziyara ta kauna. A ranar tafiya sai aka sanar da shi cewa babu
yanayi ingantacce, don haka an jirga tafiyar zuwa wani lokaci. Sai ya hau kan kwamfutarsa ya shiga shafinsa
ya fara rubutu, yana sanar da abokinsa da ke can cewa: "Kai mahaukaci, an
daga min tafiyata. Ban ji dadi ba. Ka dan jira, in kuwa ba haka ba, zan
tarwatsa Filin Saukar Jirgin Saman Robinhood, da bama-bamai." Rubuta wannan zance ke da wuya sai jami'an
tsaro masu lura da 'yan ta'adda a yanar gizo na kasar Burtaniya suka cafki sakon
da ya rubuta a shafinsa. Daga nan aka kamo shi aka gurfanar da shi a gaban
Kuliya. Shi ne mutum na farko da aka fara
cajinsa a karkashin wannan doka a kasar Burtaniya. A karshe dai Alkali ya ci tararsa tsabar kudi
Dalar Amurka 1,500, kwatankwacin N229,500 kenan a nairan Najeriya. Bayan haka,
an haramta masa shiga wannan Filin Saukan Jirgin Saman Robinhood
gaba daya, har
karshen rayuwarsa. Wani wargi wuri ya
samu!
Idan kana bakin aikinka, ka rika lura da dokokin aiki sosai, kada
ka taba bari rayuwarka ta yau da kullum ta shafi aikinka ta hanyar da bai dace
ba. Wannan shi ne abin da wani dan sanda
a birnin South Carolina na kasar Amurka ya kasa fahimta, kuma a karshe ya koyi
darasi. Watarana ya fito bakin aiki sai
ya bukaci a wanke masa mota, wato motar hukumar 'yan sanda da ke hannunsa kenan.
Da ya tashi sai ya nufi inda wasu 'yan mata ke wanke mota daga su sai rigan
nono da dan tofi. Yana tsaye a gefe suna
wanke masa mota suna ta kwarkwasa, shi kuma yana jin dadi. A cikin wannan yanayi suke wanke masa mota
ana daukan hotunansu, har da motar, da lambar motar, da kuma tambarin 'yan
sanda da ke jiki. Ana gama haka kawai
sai wadanda suka dauki wadannan hotuna kawai suka loda a shafin Facebook. Nan take hukumar 'yan sanda na kasar Amurka
ta ga wadannan hotuna, aka kamo wannan jami'i aka hukunta shi ta hanyar
sallamarsa daga aiki baki daya, domin, kamar yadda hukumar tace, wannan ya saba
wa ka'idar lura da darajar aikin 'yan sanda.
Daga cikin dadin da masu mulki ke takama da ita galibi, akwai samun
damar aikata abin da ransu ke so. Wannan
ne ya ja daya daga cikin 'yan majalisar kasar Amurka mai suna Anthony cikin
shekarar da ta gabata, lokacin da ya loda wani hoto mai dauke da shacin al'aurarsa
a shafinsa. Lokacin da majalisa ta ga
wannan hoto a shafinsa, nan take aka bukaci yayi bayanin dalilin da yayi wannan
danyen aiki, a matsayinsa na dan majalisa da ya kamata ya kare wa jama'a
mutuncinsu da nashi? Bai bayar da wani
gamsasshen dalili ba, wannan ya sa aka tilasta masa yin murabus. Yana kuka, cikin hawaye, yayi jawabin
murabus, sanadiyyar sakacin da yayi na watsar da mutumcinsa, da fallasar da ita
cikin arahar walakanci.
Daga cikin manyan katobarar har wa yau akwai al'amarin da ya faru
ga daya daga cikin manyan daraktocin kamfanin Microsoft mai suna Brayn, da ke
birnin Seatle na kasar Amurka. Yana
zaune a gidansa tare da matarsa sai 'yarsa kan kwamfuta a falo tana yin aikin
gida, ta tsaga ihu, cewa: "Abba! Me ya same ka ne…?" kafin ta karaso
ya tarbe ta. Ashe wani Dan dandatsa ne
daga cikin 'yan ta'addar yanar gizo, watau Hackers, ya shiige shafinsa na
Facebook ba tare da izini ba, ya rubuta cewa yana bukatar agajin kudi, domin ga
barayi sun kama shi sun yi garkuwa da shi, suna neman kudade masu dimbin yawa a
kasar Ingila. Alhali ga shi a zaune a
gida tare da iyalinsa. Kafin su sanar da
'yan sanda, tuni abokanansa da ke shafin suka ta tura kudade don agaza masa ko
za a sako shi, ta hanyar "Western Union Money Transfer," a karkashin
sunan da wannan Dan dandatsa ya bayar a shafin.
Daman akwai wani an ajiye wanda ke zuwa bankin kawai yana karban
kudaden, kafin daga baya aka gano cewa zamba cikin aminci ne.
Wani bawan Allah mai suna Lowell da ke jihar Massachusetts da ke
kasar Amurka ya yi hasara mafi girma a Dandalin Facebook, kafin daga baya ya
samu riba biyu. Yana da mata da suke
matukar son juna, amma tunda ta fara ma'amala a Dandalin Facebook daga nan ya
rasa kanta da mahangarta. Kullum tana
hira da jama'a, ta kasa samun lokacin maigida; daga abokananta sai
kawayenta. A haka dai daga karshe ya
fahimci lallai akwai wanda take alaka da shi, wannan ya haddasa fitina mai
girma a tsakaninsu, har a karshe aurensu ya mutu, kowa ya kama gabansa. Wannan abu ya dugunzuma masa rayuwa
matuka. Don haka ya bude wani shafi mai
suna: "FacebookCheating.com" don bayar da labarin abin da ya same
shi, da kuma baiwa jama'a da suka shiga hali irin nashi daman labarta nasu
labarin. Wannan shafi dai ya shahara,
kuma a halin yanzu har kudaden shiga yake samu ta hanyar shafin, kuma a karshe
ya sake haduwa da wata baiwar Allah a Dandalin Facebook da suka shaku, kuma ya
aure ta a halin yanzu. Kun ga ya ci riba
biyu kenan. Amma kuma, mutum nawa suka
yi hasara mara misaltuwa? Babu
iyaka. A mako mai zuwa za mu ci gaba.
Nice Blog Post !
ReplyDelete